Kamfanonin sadawar wayar salula sun yi barazanar kara kudin katin waya sanadiyyar tashin kudaden kayayyakin aikinsu da tsaron kayayyakinsu a kasarnan.

Kungiyar kamfanonin sadarwar wayar salula ta kasa, ta kuma ce tana duba yiwuwar banbanta kudaden kati ga wasu jihoshi domin kula da bukatunsu.

Kungiyar kamfanonin sadarwar wayar salula ta kasa, Kungiya ce ta manyan kamfanonin sadarwar waya da suka hada da MTN da Glo da Airtel.

Shugaban kungiyar, Gbenga Adebayo, ya gayawa manema labarai jiya a Lagos cewa tsadar, kudin mai da gas da tsaron ma’aikatansu na kawo cikas ga ayyukansu.

Yace akwai bukatar gwamnati ta kara kaimi wajen tsaron kasarnan tare da tsare lafiyar ma’aikatan sadarwar wayar salula.

Da yake magana akan jihar Kogi, shugaban yace kungiyar ta damu da rufe kayayyakin sadarwar wayar hannu a jihar sanadiyyar rashin jituwar da aka samu akan sabbin haraji da hukumar tara kudaden shiga ta jihar Kogi ta bukata.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: