Kashim Shettima Yace Tinubu Zai Gudanar Da Gwamnati Ta Kowa Da Kowa

0 91

Mataimakin shugaban kasa mai jiran gado Kashim Shettima ya yi karin haske kan abin da za a jira daga Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasar da za’a kaddamar a mako mai zuwa.

A cewarsa gwamnatin Tinubu zata kasnce ta kowa da kowa tare da bawa kowanne dan Nigeria dama domin a dama da shi

Shettima ya yi wannan jawabi ne a Abuja a yayin taron kaddamar da littafi da bayar da kyaututtuka da kuma liyafar cin abinci da aka shirya wa zababben shugaban kasa, Mataimakin zababben shugaban kasa da gwamnonin wanda kungiyyar ‘yan Arewa Women for Tinubu/Shettima’ da ‘Focus on Jagaban’ suka shirya.

Mohammed Bulama ne ya wakilci zabbabben mataimakin shugaban kasar a wajen taron.

Shugaban kungiyar dari bisa dari sai Jagaban, Dr Ibrahim Mohammed, ya yi kira ga gwamnati mai zuwa da ta ba da fifiko ga ilimi da ababen more rayuwa.

Ya ce ya kamata kuma a yi la’akari da yawan jama’a tare da jaddada bukatar samar da cikakkun bayanai. Ministar harkokin mata, Mrs Pauline Tallen, ta ce a karkashin gwamnatin Tinubu, mata zasu haskaka tare da samun cigaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: