Masarautar Hadejia Ta Baiwa Gwamna Badaru sarautar Zannan Hadejia

0 143

Mai Martaba Sarkin Masarautar Hadejia, Alhaji (Dr) Adamu Abubakar Maje CON ya nada Mai Girma Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar MON MNI a matsayin Zannan Hadejia na farko.

Wakilin Sallaman Hadejia, Alhaji Muhammad Kainuwa ne ya sanar da haka a lokacin da suka ziyarci Gwamna Badaru Abubakar a gidan gwamnati dake Dutse

Ya ce majalisar ta kudiri aniyar karrama Gwamna Badaru Abubakar da wannan kambun sakamakon jajircewar sa na ci gaban jihar da kuma masarautun musamman ta Hadejia.

Da yake mayar da martani Gwamna Badaru Abubakar ya bayyana godiya ga Allah da kuma majalisar masarautar Hadejia bisa karramawar gargajiya da aka yi masa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: