

- Gwamna Zulum ya raba wa likitoci fiye da 80 didaje da kudi Naira miliyan 79 don inganta rayuwarsu - July 2, 2022
- Manyan Sarakunan kasar Yarabawa sunyi kiran samun zaman lafiya daga gwamnati kafin zaben 2023 - July 2, 2022
- Kasar Jamus za ta fara dawo wa da Najeriya dubban kayayyakin tarihin ta da aka wawushe tun lokacin mulkin mallaka - July 2, 2022
Kimanin Mazauna Unguwar Sharadan birnin Kano 200 ne aka kwantar da su a Asibiti a jiya bayan sun shaki wani gurbataccen Sinadari wanda masu sana’ar Karafuna suka jefar.
Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya rawaito cewa an garzaya da mutanen zuwa Asibitocin Murtala Muhammad da ke Kano, da na Sharada Industrial da kuma Asibitin Ja’en.
Shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Kasa na reshen Jihar Malam Nuradeen Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Shugaban Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, Dr Hussaini Muhammad, ya ce Asibitin ya karbi Marasa Lafiya 70 wanda aka kwantar da su, inda ya ce 65 daga cikin su suna cikin wani Mayuyacin hali.
An rawaito cewa kimanin mutane 20 ne suka samu raunika bayan fashewar Iskar Gas a filin gidan da ake zuba Iskar Gas din a Jihar ta Kano.