Kimanin mutane dubu 143 ne a kasar Uganda na kasar ke cikin hadari saboda zaftarewar kasa

0 73

Jami’an Gwamnatin Kasar Uganda sun ce kimanin mutane dubu 143 ne a yankin Mount Elgon na kasar ke cikin hadari bayan zaftarewar kasa ta afkawa yankin a shekaranjiya.

Rahoton farko ya nuna cewa kimanin mutane dubu 1 ne suka rasa muhallansu a gundumar Bududa da ke yankin.

Da yawa daga cikin mutanen da lamarin ya shafa suna neman mafaka a makarantu ko gidajen makwabta da na ‘yan’uwan juna.

Ba a samu asarar rayuka ba, amma babban jami’in kula da annoba na kasar, Jimmy Ogwang ya ce an samu manyan ramuka a kasa, a kauyuka da dama, sannan ya yi gargadin cewa ruwan sama kamar da bakin kwarya da ake tafkawa a wannan daminar zai iya kara munana lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: