

Gwamna Muhammad Badaru Abubakar, ya ce kofar gwamnatin sa a bude take wajen karbar shawarwarin Al’umma domin cika Alkawarin da ya dauka a lokacin yakin neman zabe.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin Jagororin Kungiyar Ma’aikatan Kananan Hukumomi ta Kasa (NULGE) wanda suka kawo masa ziyara gidan gwamnati.