Kotu a Kasar Mali Ta Buƙaci a Dakatar da umurnin Soke Jami’iyyun Siyasa da Gwamnatin Mukin Sojin ƙasar Tayi
Wata kotu a kasar Mali ta buƙaci a dakatar da aiwatar da umurnin soke jami’iyyun siyasa da gwamnatin mukin sojin ƙasar ta yi.
Zaman kotun wanda ya gudana a gunduma ta ɗaya da ke birnin Bamako a jiya litinin, na zaman babban nasara ga jami’yyun da aka dakatar.
Rahotanni sun ce lauyoyin masu kara sun gamsar da alkalan kotun da hujjoji, abin da ya tilasta masu ja da baya.
Sai dai a ɗaya ɓangaren, alkallan kotun sun ce ba su da hurumin yanke hukuncin kan taƙaddamar da ke tsakanin jami’iyyun siyasa da ɓangaren zartaswar, yayin da suka turo shari’ar zuwa kotun ƙoli domin yanke hukunci.
Idan za a iya tunawa , a watan Mayun wanan shekarar ne gwamnatin mulkin sojin Mali ta rusa dukan jami’yyun siyasa da ke ƙasar, kamar yadda taron tattauna makomar ƙasar ya buƙaci a yi.