Kotun Ƙoli ta sanya ranar sauraron ƙarar da aka shigar kan zaɓen gwamnan jihar Kano

0 213

Kotun Ƙolin kasar nan ta sanya ranar Alhamis, 21 ga watan Disamba domin sauraron ƙarar da aka shigar kan zaɓen gwamnan jihar Kano.

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar NNPP na kalubalantar hukuncin kotun daukaka ƙara da ta tabbatar da hukuncin kotun sauraran ƙararrakin zaɓe da ta soke nasararsa tare da bayyana Nasiru Gawuna na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar na ranar 11 ga Maris.

Wannan ne karon farko da kotun za ta fara zama, inda za ta fara jin bahasi, yayin da har yanzu akwai muhimman takardun da ba a kai wa kotun ba.

Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukuncin cewa Gwamna Abba Kabir ba dan jam’iyyar NNPP ba ne a lokacin da ya tsaya takarar gwamna.

Amma tabbataccen kwafin hukuncin, wanda ya bayyana kwanaki kaɗan bayan zaman kotun, ya kunshi bayanai masu karo da juna game da hukuncin da ya janyo ce-ce-ku-ce. Duka ɓangarorin biyu dai sun yi iƙirarin cewa hukuncin ya tabbatar da nasarar da suka samu a zaben.

Leave a Reply

%d bloggers like this: