Kudirin dokar da za a cire rundunar ‘yan sandan Najeriya daga tsarin fansho na adashe ya tsallake karatu na 2

0 103

Kudirin dokar da za a cire rundunar ‘yan sandan Najeriya daga tsarin fansho na adashe, ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar wakilai.

Da yake gabatar da kudirin, wanda ya dauki nauyin kudirin ya ce jami’an ‘yan sandan da suka yi ritaya suna shiga mawuyacin hali bayan sun bar aiki.

Ya ce duk da kasancewar fanshonsu ya yi kadan idan aka kwatanta da na sauran hukumomin tsaro, tsarin fansho na adashe yana kawo cikas wajen biya.

Da yake goyon bayan kudirin, dan majalisa Shehu Koko wanda tsohon dan sanda ne, ya ce yana karbar naira dubu 23 a matsayin fansho kowane wata.

Ya ce halin da jami’an ‘yan sandan da suka yi ritaya suke ciki a kasar nan abin tausayi ne.

Bayan muhawarar, majalisar ta zartar da kudirin don karatu na biyu sannan ta mika shi ga kwamitin fansho na majalisar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: