Kasa Muhammadu Buhari ya ce kullum da matsalar tsaron da ta addabi Najeriya yake kwana yake tashi.

Ya bayyana hakan ne a cikin jawabinsa ga ’yan Najeriya albarkacin bikin Ranar Dimokuradiyya ta bana yau Lahadi.

Yayin da yake ba yan Najeriya tabbacin cewar gwamnatinsa na aiki ba dare ba rana wajen magance matsalar, ya hore yan Najeriya da su kara jajircewa da addu’o’i.

Buhari ya kuma yi bayani akan zaben 2023 mai zuwa, tare da bada tabbacin gudanar da zabe mai cike da gaskiya da adalci, ya kuma sha alwashin kubutar da dukkanin wadanda akayi garkuwa da su a fadin kasar nan.

Haka zalika ya kara bada tabbacin kawo karshen ta’addaci garkuwa da mutane, tare da kama masu aikata wadannan laifukan da zartar musu da hukunci akan lokaci.

Wannan dai na zuwa ne adaidai lokacin ake kalubalantar gwamnatin shugaban kasa muhammadu Buhari wajan gaza kawo karshen matsalar rashin tsaro a fadin kasar nan.

Ga dai fassarar wasu daga cikin muhimman batutuwan da jawabin shugaban ya kunsa ta bakin Baba Alhaji Ashbab.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: