Labarai

Kungiyar CAN ta gargadi jam’iyyun siyasa da su guji hada yan takarkarun shugaban kasa musulmi da musulmi ko kirista da kirista a zaben 2023

Kungiyar kiristoci ta kasa CAN ta gargadi jam’iyyun siyasa da su guji hada yan takarkarun shugaban kasa musulmi da musulmi ko kirista da kirsata azaben badi.

Sakataren kungiyar na kasa Barrister Joseph Bade Daramola, ya bayyana haka  a birnin tarayya Abuja, cewa hakan barazana ne zaman lafiya da hadin kan kasa.

Haka kuma ya taya dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, murna da kuma na jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar da takarar jam’iyyar Labour Party Peter Obi da sauran jam’iyyun da zasu fafata a babban zaben na 2023.

Yace kungiyar CAN na bukatar kawo dai-daito ta fuskar addini, da yanki.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: