Kungiyar dalibai ta kasa NANS reshen kudu maso gabas ta baiwa gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i ASUU wa’adin kwanaki tara na su bude dukkanin jami’o’in gwamnati.

Ko’odinetan NANS shiyyar Kudu maso Gabas, Moses Onyia, ya bayar da wa’adin ne a cikin wata sanarwa da babban mai taimaka wa kan harkokin yada labarai, Lillian Orji, ya raba a madadinsa, jiya a birnin Enugu.

Idan za a iya tunawa, ASUU, a ranar Litinin, 9 ga watan Mayu, ta tsawaita yajin aikin gargadi na watanni uku da karin wasu watannin uku. Kungiyar ta fara yajin aikin gargadi a fadin kasarnan a ranar 14 ga Fabrairu, 2022.

Sanarwar ta ce ya kamata gwamnati da ASUU su yi abin da ake bukata kafin kwanaki tara, ta kara da cewa rashin yin hakan har zuwa karshen wa’adin zai sanya dalibai daukar wani mataki mai tsauri.

A cewar sanarwar, bayan karewar wa’adin, daliban Najeriya mazauna yankin Kudu maso Gabas za su toshe gadar Neja.
11/05/20

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: