Kungiyar Daliban Kasa tayi barazanar mamaye kasa da zanga-zanga matukar gwamnatin tarayya ta cire tallafin Man fetur

0 103

Kungiyar Daliban Kasa a jiya tayi barazanar mamaye kasa da zanga-zanga matukar gwamnatin tarayya ta cire tallafin Man fetur.

Shugaban Kungiyar na Kasa Mista Sunday Asefon, shine ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya kira a Abuja.

A cewarsa, duk da cewa Kungiyar tana goyan bayan sake fasalin man fetur a kasa, amma kafin cire tallafin ya kamata a fara aiwatar da shirin kyautatawa masu karamin karfi.

Haka kuma ya ce daga cikin shirye-shiryen da gwamnati take son faraway kawo yanzu babu wanda ta aiwatar domin cire tallafin.

Saboda haka akwai bukatar gwamnatin tarayya ta dakatar da shirin na cire tallafi a yanzu.

Mista Sunday ya ce Matatun Mai 4 da ake dasu a kasar nan, babu wanda yake aiki, kuma koda suna aiki basa samar da abinda ake Tsammani daga wajen su.

Kazalika, ya ce gwamnatin tarayya bata tuntubi masu ruwa da tsaki ba, kafin yunkurin cire tallafin man fetur din.

Leave a Reply

%d bloggers like this: