Kungiyar IPOB tayi biyayya ga gwamnatin tarayya inda ta soke dokar zaman gida a yankin Kudu maso Gabas

0 61

Haramtacciyar kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB, tayi biyayya ga gwamnatin tarayya, inda ta soke dokar zaman gida a yankin Kudu maso Gabas.

Kungiyar ta fuskanci tofin Allah tsine da zargin zagon kasa ga dimokuradiyya, walwalar jama’a da kuma tada kayar baya a yankin.

Kakakin kungiyar, Emma Powerful, a jiya ya ce an soke dokar zama a gida domin bai wa jama’ar jihar Anambra damar shiga zaben gwamna a gobe.

A wani abin da ya zama kamar kashedi ga masu tada kayar bayan IPOB, ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya ce zai hukunta wadanda suka tayar da rikici a lokacin zaben Anambra.

A wani labarin kuma, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana cewa ‘yan Najeriya suna fama da bakin talauci, rashin tsaro, koma baya da kuma rashin shugabanci na gari a cikin ‘yan shekarun da suka gabata na mulkin dimokradiyya.

Atiku ya bayyana haka ne a jiya a Arewa House, Kaduna, yayin da yake jawabi a matsayin babban bako a taron lacca na kasa da Arewa Media and Development Forum ta shirya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: