Kungiyar masu dillancin man fetur ta Najeriya IPMAN ta janye matsayarta ta sayar da litar mai daga naira 180 zuwa sama

0 75

Kungiyar masu dillancin man fetur a Najeriya IPMAN ta janye matsayarta ta sayar da litar mai daga naira 180 zuwa sama.

A yanzu IPMAN ta ce za ta hakura ta ci gaba da sayar da shi a kan farashin gwamnati na naira 165.

A ganawa da manema labarai ranar Laraba a Abuja, Shugaban kungiyar Chinedu Okoronkwo ya ce hukumar PPMC ta amsa musu bukatun da suka gabatar.

A kan haka ya bukaci ‘yan Najeriya da su daina fargabar fuskantar karancin man fetur a gidajen man.

Mr Okoronkwo ya kara da cewa yanzu haka ana loda man daga Legas zuwa sauran yankunan kasar, kuma yana sa ran nan gaba kadan za a daina dogayen layuka a gidajen man a fadin kasar.

A baya IPMAN reshen jihar Legas ta bayyana cewa ba za ta iya sayar da mai kasa da naira 180 a duk lita, bayan da ta ce yanayin yadda take kashe kudi kafin sauke man a gidaje ya karu sosai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: