Kungiyar Matasan Arewa maso Gabashin Najeriya ta yi Allah-wadai da kisan da aka yi wani mutum

0 207

Kungiyar Matasan Arewa maso Gabashin Najeriya ta yi Allah-wadai da kisan da aka yi wani mutum a garin Nayi-nawa da ke karamar hukumar Damaturu ta jihar Yobe, wanda har yanzu ba san wadanda suka aikata laifin ba.

Kungiyar ta bayyana damuwar ta ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban daraktan ta, Dauda Muhammad Gombe tare da mikawa manema labarai a Damaturu.

Yayin da yake jajantawa iyalan mamacin, kumgiyar ta bukaci jami’an tsaro da su kara kaimi wajen ganin an shawo kan wannan mummunar dabi’a a cikin birnin. Babban Darakta na kungiyar ya tabbatar da cewa kungiyar ta himmatu wajen bayar da tallafin da ya dace domin mara baya ga kokarin masu ruwa da tsaki a matakai daban-daban.

Leave a Reply

%d bloggers like this: