Kungiyar NAWOJ sun taya Zainab Shua’ibu Rabo murnar zama Babbar mai taimaka wa gwamna kan harkokin yada labarai

0 233

Sabuwar shugabar kungiyar mata ‘Yan jaridu ta kasa reshen jihar Jigawa Aisha Ilyasu Abubakar, ta mika sakon taya murna da Zainab Shu’aibu Rabo bisa nadin da gwamnan Malam Umar ya mata a matsayin Babbar mai taimaka masa kan harkokin yada labarai.

Shugabar kungiyar ta NAWOJ ta mika sakon godiyar ta ga gwamna Malam Umar Namadi bisa yin la’akari da namjin kokarin Zainab Shua’ibu Rabo tare da nada wannan matsayi.

Kazalika, Sakatariyar kungiyar Salamatu Nuhu, da sauran mambobin na kungiyar ta NAWOJ sun mika nasu sakon taya murnar ga Zainab Shu’aibu Rabo. Sun kuma yi mata fatan nasara da fatan zata yi aiki tukuru da zai sa ta zamo abin koyi ga yan baya.

A matsayinsu na ‘yan kungiyar NAWOJ, suna alfahari da irin nasarorin da ta samu, kuma suna fatan ganin irin gagarumar gudunmawar da za ta bayar a fannin yada labarai da kuma ci gaban jihar Jigawa baki daya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: