Kungiyar Save the Children tare da Glazo Smith Kline sun bada gudunmawar na’urorin aikin asibitin na fiye da miliyan 55 ga gwamnatin jihar Jigawa

0 85

Kungiyar kyautata rayuwar kananan yara ta Save the children tare da hadin gwiwar Glazo Smith Kline sun bada gudunmawar na’urorin aikin asibitin da kudin su ya haura naira miliyan hamsin da biyar ga Gwamnatin Jihar Jigawa.

Babban jami`in shirin kungiyar Dakta Adamu Isah yace na`urorin sun kunshi na taimakawa marasa lafiya wajan yin numfashi wato Oxygen da kudinsu ya kai naira miliyan arba`in da bakwai, yayin da suka horas da jami`an lafiya akan kudi kusan naira miliyan takwas.

Yace shirin ya sami amincewar fadada ayyukansa zuwa dukkanin manyan asibitocin dake jihar nan.

Dakta Isah ya kara da cewa asibitocin da suka amfana da gudunmawar sune na garuruwan Babura da Hadejia da Gumel da kuma Kazaure.

Da yake karbar gudunmuwar babban sakatare a ma`aikatar alfiya, Dakta Salisu Mu`azu ya bada tabbacin yin amfani da na`urorin kamar yadda ya kamata.

Babban sakataren wanda ya sami wakilcin Daraktan lura da asibitoci na ma`aikatar, Dakta Bashir Ahmad ya bada tabbacin gwamnatin jiha na cigaba da kyautata dangantaka tsakaninta da abokan hadin gwiwa na samar da cigaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: