Labarai

Kungiyar SERAP tayi kira ga shugaba Buhari da ya kara nazari domin janye afuwar da aka yi wa tsaffin gwamnonin jihohin Filato da Taraba

Kungiyar SERAP mai fafutukar yaki da cin hanci da rashawa da tabbatar da shugabanci na gari ta yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya kara Nazari, domin janye afuwar da aka yi wa tsaffin gwamnonin Jihar Filato, Sanata Joshua Dariye, da kuma Rabaran Jolly Nyame na Jihar Taraba, wadanda ke zaman gidan yari bisa laifin cin hanci da rashawa.

Idan dai za’a iya tunawa Majalisar magabata ta kasa da shugaban kasa ya jagoranci zamanta a makon da ya gabata ta yi afuwa ga wasu mutane 159 da ake zargin su da laifi cin amanar kasa.

Daga cikin su akwai Dariye da Nyame da aka daure su a gidan yari bisa samun su da laifin satar naira miliyan dubu 1,160 da kuma naira miliyan dubu 1,600.

A cikin wasikar a ranar Asabar mai dauke da sa hannun mataimakin daraktan SERAP, Kolawole Oluwadare, kungiyar ta bukaci gwamnati da ta yi karin haske, kan ko afuwar da aka yi wa Dariye da Nyame zai ba su damar mayar da kadarorin da aka sace wanda mallakar ga gwamnati ce.

SERAP ta ce a bayyanae yake, yafewar ya sabawa ka’idojin kundin tsarin mulkin kasa, da kuma wajibcin da kasar ta rataya a wuyan kasa da kasa ciki har da yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da cin hanci da rashawa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: