Kungiyyar ASUU zasu tattauna domin dakile yunkurin da kungiyyar takeyi na sake shiga wani sabon yajin aiki

0 68

Kungiyyar malaman Jami’oi ta kasa ASUU da gamayyar kungiyyar jami’an gwamnatin tarayya zasu tattauna a makon nan domin dakile yunkurin da kungiyyar takeyi na sake shiga wani sabon yajin aiki.

Kawo yanzu dai ba’a bayyana lokaci da ranar da zasu zauna ba, amma an gano cewa jami’an gwamnatin da suka hada da minsitan ilimi da na kwadago da kuma wasu manyan jami’an gwamnati ne zasu tattauana da malaman.

Shugaban kungiyyar ASUU na shiyyar Legas Dr Adelaja Odukoya a lokacin dayake tattaunawa da manema labarai a jiya lahadi, ya tabbatar da cewa a wannan makon zasu zauna da mukararraban gwamnatin tarayyar.

Kafin hakan dai a ranar 23 ga watan Disambar 2020 ne kungiyyar ASUU ta janye yajin aikin data shafe watanni 9 tana gudanarwa, bayan gwamnatin tarayya tayi alkawarin biyan kungiyyar Naira Biliyan 40 domin farfado da jami’o’in kasar nan da kuma alkawarin biya musu wasu daga cikin bukatun su.

Inda gwamnatin ta alakanta jinkirin biyan kudaden ga mahukuntan babban bankin kasa CBN.

Leave a Reply

%d bloggers like this: