Kwamishinan ilimi na jihar Bauchi ya bayyana cewa ansamu kimanin dalibai dubu 15 da satar amsar jarrabawa a jihar

0 84

Kwamishinan ilimi na jihar Bauchi Dr Aliyu Usman Tilde, ya bayyana cewa ansamu kimanin dalibai dubu 15 da satar amsar jarrabawar da hukumar ilimi matakin farko ta jihar ta shiryawa daliban ajin karshe na makarantar karamar sakandire.

Dr Tilde ya bayyana hakan a lokacin  dayake zantawa da manema labarai a jiya Laraba a birnin Bauchi, inda yace kimanin dalibai dubu 52 ne suka zana jarrabawar, kafin gwamnan jihar Sanata Bala Mohammed ya rushe majalissar zatarwarsa.

Amma a cewar kwamshina jihar, ansamu mummunan satar amsar jarrabawa, musamman a tambayoyin chanki chanki.

Ya kara da cewa, sun kuma gano cewa, mafi akasarin daliban, wasu daga cikin malaman su ne, suka basu amsa.

Sun kuma gano hakan ne bayan sun bibiyi wasu daga cikin makarantun, inda suka gano cewa, wasu daliban sun kwafi ansoshin yan’uwansu dalibai.

Leave a Reply

%d bloggers like this: