Majalisar dokokin jihar Jigawa ta yabawa gwamnatin jiha saboda ware kudade domin gudanar da ayyukan mazabu

0 77

Majalisar dokokin jihar Jigawa ta yabawa gwamnatin jiha saboda ware kudade naira miliyan dubu uku da miliyan dari biyu kowacce shekara domin gudanar da ayyukan mazabu a dukkan mazabu 30 da ke fadin jihar nan.


Shugaban majalisar, Alhaji Idris Garba, ya yi wannan yabo lokacin da yake mayar da jawabi dangane da gabatar da kiyasin kasafin kudin sabuwar shekarar ta 2022 da gwamna Muhammad Badaru Abubakar ya gabatarwa zauren majalisar.


Ya lura cewa gwamnatin jiha ta zuba naira miliyan dubu 19 da miliyan 200 wajen gudanar da ayyukan mazabu cikin shekaru shida wadda hakan ya yi tasiri wajen inganta tattalin arziki da zamantakewar al’ummar jihar nan.


Alhaji Idris Garba ya kuma bayyana cewa ganin haka ne majalisar ta bullo da wasu sabbin dabarun da za su kawo ingancin wajen tsare-tsare da kuma gudanar da ayyukan mazabu domin kammala su cikin kasafin kudin kowacce shekara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: