Shugaba Buhari ya yabawa shugaban Kasar Faransa kan fadada harkokin kasuwanci tsakanin kasar Najeriya da Faransa

0 55

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yabawa shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron akan fadada harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu, yayin da ya jaddada hadin kan Najeriya da kasar wajen murkushe kungiyoyin ‘Yan ta’adda.

Shugaba Buhari ya bayyana kanan ne, a lokacin da ya ziyarci fadar shugaban Faransa inda ya gana da shugaba Macron,

Buhari yace ziyarar da Macron ya kai Najeriya ta bude kofofin ci gaba ta hanyar sana’oi, yadda harkokin kasuwanci suka habaka, musamman kafa kungiyar zuba jari tsakanin kasashen biyu.

Haka kuma ya yabawa Faransa bisa taimakawa kasashen afrika da rigakafin cutar corona miliyan 10 a 2020

Dangane da batun tsaro kuma, Shugaba Buhari ya jinjinawa Faransa akan aniyar ta na tabbatar da zaman lafiya a yankin Sahel da kuma Yankin Tafkin Chadi, wadanda suka taimaka wajen yaki da ta’addanci da kuma tsatsauran ra’ayi.

Buhari yace Najeriya da Faransa na da damar fadada dangantakar su ta hanyar tintibar juna a matakin ministoci, yayin da ya bayyana kasar a matsayin abokiyar tafiya dangane da ci gaban kasashen Afirka.

Leave a Reply

%d bloggers like this: