Kwamitin albarkatin man fetir na jihar Jigawa, yace gidajen sayar da man fetir 12 ne suka sami man fetir a jiya Laraba a fadin jihar Jigawa.

A sanarwar da kwamitin ya bayar, tace gidajen man sun sami adadin man fetir da ya kama daga lita dubu 36 zuwa wadanda suka samu lita dubu 40 da wadanda suka samu lita dubu 45 da kuma wadanda suka samu lita 50.

Gidajen man da suka sami man fetir din sun hadar da Mega Station Dutse da ya samu lita dubu 76, da gidan mai na Shidde dake garin Taura da gidan mai na AS Liman a Hadejia da gidan mai na ASG PET a Kiyawa da gidan mai na Babandoki a Ringim da gidan mai na sabon Garin ‘Ya’ya da gidan mai na Nushe dake Kirikasamma da gidan mai na Nuriyya Global dake Babura.

Sauran gidajen man da suka samu man fetir sun hada da Gudunya SA Kanya dake garin Babura da AU Jeme dake Kazaure da gidan mai na NU Synergy a Ringim da kuma gidan mai na UIG PET a Shuwarin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: