Majalisar dattawa zartar da wani kudirin doka da ke neman yin gyara ga dokar halatta kudaden haram ta 2011.

Gyaran da aka gabatar a kudirin ya sa ya zama wajibi bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudi su bayar da rahoton duk wata hada-hadar kudi da ya haura naira miliyan 5 ga wani mutum, da kuma naira miliyan 10 ga kowane kamfani.

Za a yi wannan rahoton ne a rubuce sannan a aika da shi zuwa sashin da aka ware da ke yaki da safarar kudade dake karkashin Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC).

Abdu Kwari na jam’iyyar APC daga jihar Kaduna ne ya dauki nauyin kudirin dokar.

Amincewar kudirin ya biyo bayan nazarin rahoton kwamitin yaki da cin hanci da rashawa.

Kafin a amince da kudirin a jiya, wanda ya dauki nauyin kudirin ya ce zai taimaka wajen yaki da cin hanci da rashawa, halasta kudaden haram da kuma ta’addanci.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: