Kwamitin kare hakkin mai saye da sayarwa na jihar Jigawa ya kama wani dan tireda da laifin yin algus a bahuna 23 na kayayyakin abinci.

0 80

Kwamitin kare hakkin mai saye da sayarwa na jihar Jigawa yace ya samu nasarar kama wani dan tireda mai suna Nuhu Isyaku dan karamar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano da laifin yin algus a bahuna 23 na kayayyakin abinci.

Shugaban kwamitin, Farouk Abdallah Mallam Madori yace sun kama mutumin ne a kasuwar Babura a wata ziyarar bazata da suka kai kasuwar.

Farouk Abdallah yace an kama mutumin ne dauke da bahunan gero 17 da aka yiwa algus da kuma bahuna wake 6 suma da aka yiwa algus.

Yace kotun tafi da gidanka ta yanke masa hukuncin daurin watanni 6 ko kuma zabin biyan tarar naira dubu 80.

Ya tabbatar da cewa kwamitin zai cigaba da sanya ido a kasuwanni domin kare masu sayayya wajen sayen kayayyakin da aka yiwa algus.

Leave a Reply

%d bloggers like this: