Lokaci kawai muke jira mu tsunduma yajin aiki da kuma gagarumar zanga-zanga

0 681

Kungiyar kwadago ta NLC ta musanta batun sabawa umarnin kotu dangane da yajin aikin sai baba ta gani da zata tsunduma a ranar Talata mai zuwa.

An bayar da rahotan kungiyar na mayar da martani dangane da kalaman babban lauyan gwamnati kuma Ministan shari’a na kasa Lateef Fagbemi daya bayyana matakin nasu a matsayin bujirewa umarnin kotu, kungiyar tana mai cewa hakan bashi da wata makama a kundin tsarin mulki.

Kungiyar tace a shirye take lokaci kawai ake jira domin dakatar da harkkokin aiki yayin yajin aikin da kuma gagarumar zanga-zangar adawa da cire tallafin man fetur da karuwar kudin lantarki, hauhawar farashi da tsadar rayuwa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: