‘Yan bindiga sun hallaka mutane 6 da kuma raunata wasu 4 a jihar Kaduna

0 217

Akalla mutane 6 ne aka hallaka yayin mutum 4 suka tsira da raunuka yayin wani hari da yan bindiga suka kai kauyen Takanai dake karamar hakumar Zangon Kataf a jihar Kaduna.

Hakumar yansanda a jihar har yanzu bata tabbatar da aukuwar lamarin ba, amma mazauna yankin sun sanar da yan jarida cewa, an kai harin ne ranar Talata da dare, a garin mai tazara kadan da shingen binciken sojoji dake kan titi kusa da kauyen Juju mahaifar shugaban hafsan tsaro na kasa janar Christopher Musa.

Wani mai shuna Sam Achi yace yan bindigar sun mamaye kauyen da misalin karfe 7 na yammaci sannan suka budewa wasu gidaje 2 wuta, lamarin da yayi sanadin rayukan mutane 6 da jikkata wasu 4.

Achi yace yan bindigar sun kwashe sama da sa’a guda suna gudanar da ayyukansu kafin isowar jami’an tsaro. Sam Achi wanda ya kasance shugaban kungiyar cigaban yankin ne yayi kira ga gwamnati da hakumomin tsaro da su dauki matakan magance matsalar tsaro a kudancin Kaduna cikin gaggawa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: