Lauyoyin Atiku sun shigar da kara suna kalubalantar zuwan Tinubu Jami’ar jihar Chikago

0 285

Tawagar lauyoyin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP Atiku Abubakar sun shigar kara suna kalubalantar bulaguron shugaban kasa Bola Tinubu zuwa jami’ar jihar Chikago domin hana sakin takardun karatunsa.

Mataimaki na musamman ga Atiku kan harkokin sadarwa Prank Shuaibu ya bayyana haka ga jaridar Punch, cewa tawagar lauyoyin zasu martani bayan kusan sa’o’I 48 kan karar a kotun Amurka.

Tun da farko dai Atiku ya samu sahalewar kotun domin samun bayanan karatun shugaban kasar ga lauyoyinsa.

Maisharia Jeffrey Gillbert a makon daya gabata ya bayar da umarnin sakin bayanan karatun cikin kwanaki.

Atiku dai na kalubalantar nasarar tsohon gwamnan jihar a zaben 2023, da kuma hakucin kotun saurarar kararrakin zaben shugaban kasa.

Bayanan da dan takarar jam’iyyar PDP ya samu, ta hannun lauyoyinsa, sun hada da tarihin shigar sa jami’ar, da kuma bayanan ranar da ya fara karatu, bayanan yau da kullum, da kyaututtuka da Bola Tinubu ya lashe da sauran abubuwa. Sai dai a yau alhamis ne wa’adin da mai shari’a Gilbert ke karewa, lauyoyin shugaban kasa Tinubu sun garzaya Maldonado inda suke rokon soke hakuncin mai shari’a Gilbert da ya bayar da damar dubawa da kuma bincikar tarihin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: