Ma’aikatan Wucin Gadin Hukumar Kidaya Fiye Da 467 Ne Sukayi Zanga-Zanga Kan Rashin Biyan Su Alawus-alawus
Kimanin ma’aikatan wucin gadi 467 na hukumar kidaya ta kasa reshen jihar Bauchi ne suka fito kan tituna domin nuna rashin amincewarsu da rashin biyansu alawus-alawus.
An gudanar da zanga-zangar ne a titin Wunti dake cikin birnin Bauchi a jiya.
ma’aikatan wucin gadin na dauke da alluna masu dauke da rubutu daban-daban.
Kakakin ma’aikatan na wucin gadi, Abbas Adamu, a lokacin da yake zantawa da darakta da ma’aikatan hukumar na jihar Bauchi, ya ce sun yi aikinsu amma har yanzu basu samu alawus alawus din su ba.
A cewarsa, sun rubuta takardun korafi da dama zuwa ga ofishin hukumar na jiha da ya biya wadanda basu samu kudinsu ba daga cikin masu bayar da horo da masu ayyuka na musamman, amma basu samu martanin da zai karfafa musu gwiwa ba.
Da yake mayar da martani, daraktan hukumar na jiha Hudu Baballe, ya yabawa ma’aikatan wucin gadin bisa yadda suka gudanar da zanga-zangar cikin lumana ba tare da tashin hankali ba.