Ma’aikatar Kare Muhalli ta jiha ta kiyasta kashe kudi Naira miliyan dubu shida wajen gudanar da manyan ayyuka a jihar Jigawa

0 73

Ma’aikatar Kare Muhalli ta jiha ta kiyasta kashe kudi naira miliyan dubu shida wajen gudanar da manyan ayyuka na yau da kullum a shekara mai zuwa.

Mukaddashin babban sakataren ma’aikatar, Alhaji Bello Idris ne ya sanar da haka lokacin da yake kare kasafin kudin ma’aikatar na shekara mai zuwa a gaban kwamatin kula da muhalli na majalisa.

Ya ce daga cikin adadin kudin an ware naira miliyan dubu biyar da miliyan dari shida da goma ga ma’aikatar, sai naira miliyan dari da casa’in na hukumar tsaftar muhalli ta jiha da kuma naira miliyan dari biyu da talatin da bakwai wanda aka tsara kashewa a hukumar samar makamashi ta jiha.

Alhaji Bello Idris yayi bayanin cewa zasu bada kulawa ta musamman ga hana kwararowar Hamada da zaizayar kasa da Tarawa da kwashe shara da kuma renon irin bishiyoyi.

A nasa jawabin shugaban kwamatin muhalli na majalisar, Alhaji Usman Alto Roni ya bayyana gamsuwa bisa nasarorin da ma’aikatar da kuma hukumomin suka samu a wannan shekarar mai karewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: