Majalisar Dattijai ta amince da mutanen da shugaban kasa Buhari ya tura don naɗawa Ministocin cike gurbi

0 133

Majalisar dattijan Najeriya ta amince da sabbin ministoci bakwai da shugaba Muhammadu Buhari ya tura ma ta domin tabbatar da naɗinsu.

An tabbatar da naɗin ne bayan zaman tantace su da majalisar ta yi a zamanta na wannan Larabar.

Yayinda wasu daga cikin sabbin ministocin, musamman tsohon ɗan majalisa, da aka bukaci su yi gaisuwar majalisa su wuce, wasu daga cikinsu an tsare su da tambayoyi kan abubuwan da ya shafi kasa.

Shugaba Buhari, a wata wasika da ya aikewa majalisa mai dauke da kwanan watan 15 ga watan Yuni, 2022, ya bukaci majalisar ta amince da naɗinsa.

Ya ce neman bukatar amincewa da naɗin ya yi daidai da tanadin kudin tsarin mulki sashi na 147(2) na kudin tsarin mulkin shekara ta 1999 na Tarayyar Najeriya, da aka yiwa kwaskwarima.

Ministocin da aka tabbatar da naɗin nasu sun haɗa da: Henry Ikechukwu Ikoh – daga Abia; Umana Okon Umana – daga Akwa Ibom; Ekumankama Joseph Nkama- daga Ebonyi; da Goodluck Nanah Opiah – daga Imo.

Sauran su ne Umar Ibrahim El-Yakub – daga Kano; Ademola Adewole Adegoroye – daga Ondo; da Odum Udi – daga Rivers.

Leave a Reply

%d bloggers like this: