Majalisar Zartarwa ta tarayya ta amince da ayyukan inganta wutar lantarki a Najeriya

0 78

Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da ayyukan inganta wutar lantarki a fadin kasar nan.

Ministan Wutar Lantarki, Abubakar Aliyu, shine ya bayyana hakan ga manema labarai na fadar shugaban kasa bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya wanda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta a jiya a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Abubakar Aliyu ya ce za a gudanar da ayyukan ne da nufin karfafa kamfanin watsa wutar lantarki na kasa da kuma kara samar da wutar lantarki a kasarnan.

Ministan ya ce bukata ta biyu kuma, ita ce ta sayo taransfomar wutar lantarki da kayan aikin domin kamfanin watsa wutar lantarki na kasa da nufin zuwa wurare shida.

Abubakar Aliyu ya ce Yan-tada kayar baya sun lalata babban layin da ya kai wutar lantarki zuwa Maiduguri.

Ya ce sau da dama ma’aikatar wuta ta na kokarin gyara layin amma sai Yan-tada kayar baya su koma su sake lalatawa.

Ya ce, a halin yanzu, dan kwangilar ya dawo domin aikin gyara babban layin da aka lalata a baya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: