Majalisar Dokoki ta Yobe ta gudanar da sauraron Ra’ayoyi kan kudurin dokar gwajin Genotype da Hepatitis kafin Aure
Majalisar dokoki ta jihar Yobe ta gudanar da sauraron ra’ayoyin jama’a kan kudurin dokar da ke neman wajabta gwajin jini na genotype da cutar hepatitis kafin auren ma’aurata a fadin jihar.
Wannan kuduri na da nufin gyara dokar hana nuna wariya ta shekarar 2014, tare da ƙarfafa yaki da cututtukan sankarau da hepatitis.
Da yake jawabi a wajen taron da aka gudanar a Damaturu, shugaban majalisar, Ciroma Mashio, ya ce dokar za ta taimaka wajen rage barazanar lafiyar jama’a da cututtukan ke haddasawa idan aka zartar da ita. Ya ce an gudanar da sauraron ra’ayoyin a biranen Gashua, Potiskum da Damaturu domin tattara bayanai daga matakin ƙasa da za su taimaka wa majalisar wajen tsara doka mai nagarta da tasiri.
Honourable Mashio ya yabawa kwamitin lafiya na majalisar kan kokarinsu na shirya zaman da kuma kungiyar Sickle Cell Disease Eradication Initiative (SICKDEI), wacce ta fara da kawo wannan kuduri. Ya kuma jinjina wa Gwamna Mai Mala Buni kan goyon bayansa ga majalisar domin ganin an samu nasarar shigar da kudurin doka.