Labarai

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta ce ta aika wa mataimakin gwamnan jihar Mahdi Aliyu Gusau sanarwar cewa za ta tsige shi daga mukaminsa

Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta ce ta aika wa mataimakin gwamnan jihar Mahdi Aliyu Gusau sanarwar cewa za ta tsige shi daga mukaminsa.

Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar Shamsudeen Hassan ya shaida wa tashar talabijin ta Channels wannan labarin a Gusau, babban birnin jihar.

Ya ce majalisar za ta tsige mataimakin gwamnan daga mukaminsa ne saboda tuhumar da suke yi masa cewa ya aikata laifuka karkashin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Majalisar ta kuma tuhumi Mahdi Aliyu Gusau da azurta kansa da kudin al’umma ta haramtacciyar hanya bayan da ta ce ya karkatar da kudaden jihar ga wasu bukatun kansa, baya ga kitsa wani shiri na damfarar jihar.

Yayin da mataimakin gwanan ke cewa bai aikata wani laifi ba, majalisar ta ce ta aika wa Mahdi Aliyu Gusau sanarwar tsige shin ta hannun sakataren gwamnan jihar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: