Majalisar Masarautar Kazaure da ke jihar Jigawa ta raba kayayyakin abinci da dabbobi na kudi kimanin Naira miliyan 12 ga mabukata

0 19

Majalisar Masarautar Kazaure da ke nan Jihar Jigawa ta raba kayayyakin Abinci da Dabbobi na kudi Kimanin Naira Miliyan 12 da Dubu 2,720 ga Mabukatan yankin.

Kakakin Masarautar Malam Gambo Garba, shine ya sanar da hakan ga manema labarai a Dutse.

A cewarsa, an raba kayayyakin ne mutanen da suka fito daga Karkarna cikin Gundumar Yankwashi.

A jawabinsa, Mai Martaba Sarkin Kazaure Alhaji Najib Hussaini, ya yabawa wadanda suka bada Zakkar domin tallafawa Mabukata.

Sarkin wanda ya samu wakilcin Makaman Kazaure Malam Jamilu Umaru, ya bukaci wadanda aka bawa tallafin su yi amfani da su ta hanya mai kyau domin rage radadin talauci.

Kazalika, Sarkin ya bukaci Iyayen da suke yankin su tura yaran su zuwa Makaranta.

Leave a Reply

%d bloggers like this: