Majalisar wakilai na binciken kwakwaf akan bashin kusan tiriliyan 3 da gwamnatin Najeriya ke bin kamfanonin mai

0 94

Majalisar Wakilan Najeriya ta ƙaddamar da bincike ranar Talata kan kuɗi fiye da naira tiriliyan biyu da rabi da gwamnatin ƙasar ke bin kamfanonin man fetur 77 bashi.

Rahoton jaridar Punch ya ce ‘yan majalisar na aiki ne da wani rahoton shekarar 2019 da kwamatin Nigeria Extractive Industry Transparency Initiative ya gabatar.

Kakakin Majalisa Femi Gbajabiamila ya yi barazanar cewa majalisar za ta yi amfani da tanadin kundin tsarin mulki a kan duk kamfanin da ya ƙi bai wa binciken haɗin kai.

“Don nuna muhimmancin wannan aikin, bari na tabbaatar muku cewa idan aka samu wani mutum ko kamfani da ya ƙi bai wa binciken haɗin kai, zai zama lokaci na farko da majalisa ko kuma ni zan yi amfani da ikon kundin tsarin mulki don a kama shi,” in ji Mitsa Gbajabiamila.

Ya ƙara da cewa naira tiriliyan 2.6 kuɗi mai yawa da bai kamata a ƙyale su tafi a banza ba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: