

- Mataimakin Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, shine ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar APC - May 27, 2022
- Shugaba Buhari yace gwamnatinsa tana assasa ginshiki mai inganci na kyakykyawar rayuwa domin yara manyan gobe a Najeriya - May 27, 2022
- Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta haramta bangar siyasa da tare da yin amfani da duk wani makami ga yaran yan siyasa - May 27, 2022
Majalisar wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya ta kaddamar da fara cikakkiyar aiwatar da kudirin iskar gas na kasa da zummar dakile hauhawar farashin gas din girki.
Majalisar ta amince cewa dole gwamnati ta sanya baki domin rage farashin gas din girkin a Najeriya.
Matakin ya biyo bayan amincewa da kudirin da Rotimi Ogunsoye na jam’iyyar APC daga jihar Lagos ya gabatar a zauren majalisar a jiya.
A kudirin nasa, Rotimi Agunsoye ya koka bisa karuwar farashin gas din girki a shekarar da ta gabata, inda yayi nuni da cewa samun ninkin farashin gas din girki ba abu ne da ya dace da cigaban tattalin arziki ba.
Yace kudirin iskar gas na kasa na da damar kara yawan amfani da gas din girki a gidaje kuma yana da amfani sosai a bangaren tattalin arziki wanda ka iya rage farashinsa domin mutane su iya saya.
An dorawa kwamitin gas ya kula da aiwatar da kudirin tare da bayar da rahotonsa ga majalisar cikin makonni 4.