Majalisar wakilai ta gayyaci ministan babban birnin tarayya da ya gurfana gaban kwamitinta kan tabarbarewar tsaro

0 42

Majalisar wakilai ta gayyaci ministan babban birnin tarayya, Mohammed Bello, da ya gurfana gaban kwamitinta na bai daya, kan tabarbarewar tsaro a yankin.

Matakin dai ya biyo bayan kudirin gaggawa da mataimakin shugaban marasa rinjaye, Toby Okechukwu ya gabatar a yau.

A kudirin nasa, ya ce Abuja ba ta taba samun irin wannan rashin tsaro ba, inda ya ce rashin tsaro ya samo asali ne sakamakon shigowar ‘yan fashin daji da sauran miyagun mutane, da rashin samar da kayayyakin tsaro na zamani a tsakiyar birnin da garuruwan dake kewaye da birnin, da rashin kula da wadanda ake da su, da suka hada da kyamarar CCTV da fitilun kan titi.

Ya koka kan yadda ake tafiyar da birnin tarayya a karkashin jagorancin Ministan.

Yayin da yake yanke hukunci kan lamarin, Kakakin Majalisar, Femi Gbajabiamila, ya ce kwamitin babban birnin da kwamitin bai daya na majalisar, na iya aiki kafada da kafada dangane da matsalar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: