Wasu ‘yan bindiga sun sace ma’aikatan karamar hukumar Zariya su 13 ta jihar Kaduna

0 73

Wasu ‘yan bindiga sun sace ma’aikatan karamar hukumar Zariya su 13 a jihar Kaduna a lokacin da suke tafiya a cikin wata mota.

Lamarin ya faru ne jiya da karfe 5 na yamma a tsakanin Giwa da Zariya.

Majiyoyi sun shaidawa manema labarai cewa, masu garkuwar sun kyale direban domin kai rahoto ga helkwatar karamar hukumar da iyalan wadanda aka sace.

An rawaito cewa daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su akwai wasu maza hudu da suka hada da Dalhatu Awai, Sulaiman Zailani, Nura Abdullahi da Umar Shehu.

Matan da aka sace sun hada da Deborah Mugu, Halima Tabari, Fatima Abdullahi, Hafsat Zakari da Maryam Fatika.

Sauran sun hada da Huwaila Fate, Hajara Mohammed, Kuluwa Isah da Amina Sulaiman.

Ba a samu jin ta bakin kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, Mohammed Jalige, ba, har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Leave a Reply

%d bloggers like this: