Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta musanta rahotannin da ke cewa ‘yan bindiga na kakaba dagatai a kauyukan jihar

0 79

Rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto ta musanta rahotannin da ke cewa ‘yan bindiga na kakaba dagatai a kauyukan jihar.

Akwai rahotannin da ke cewa ‘yan bindiga sun zabi shugabannin gargajiya a Sabon Birni, kauyen da yake fama da hare-hare a ‘yan kwanakinnan.

Sai dai a wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Sanusi Abubakar ya fitar, yace an gudanar da bincike kan wannan labarin kuma an gano ba gaskiya bane.

Ya kuma bayyana cewa jami’an tsaro na gudanar da ayyuka domin dawo da zaman lafiya a yankunan da ‘yan fashin suke aika-aika a jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: