Marasa Lafiya Na Jiran Tsammani Bayan Da Likitoci Masu Neman Kwarewa Suka Shiga Yajin Aiki A Jihar Jigawa

0 74

Majinyata a jihar Jigawa a jiya sun shiga cikin kunci bayan da likitoci masu neman kwarewa na asibitocin tarayya biyu dake jihar suka shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyar da kungiyarsu ta fara.

Masu aiko da rahotannin da suka ziyarci manyan asibitocin guda biyu domin sanin halin da ake ciki dangane da yajin aikin, sun lura cewa likitocin suna asibitoci amma ba sa kula da marasa lafiyar.

A Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya da ke Birnin Kudu, likitoci sun kasance a dakunansu na hutawa yayin da marasa lafiya ke cikin dakunan tuntuba suna zaman jira.

Shugaban kungiyar reshen asibitin, Dokta Shamsuddin Haruna Ubale, ya ce sun shiga yajin aikin gargadi ne bisa bin umarnin hedikwatar kungiyar ta kasa. Sai dai duk kokarin da aka yi na yin magana da mahukuntan asibitin kan yajin aikin da ke gudana ya ci tura.

Leave a Reply

%d bloggers like this: