Femi Gbajabiamila Ya Dage Zaman Majalisar Wakilai Har Zuwa Wani Lokaci Saboda Fargabar Tsige Shi

0 80

Kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila Ajiya ya dage zaman majalisar har zuwa wani lokaci saboda fargabar yiwuwar ‘yan majalisar za su tsige shi.

Femi Gbajabiamila, wanda ya jagoranci zaman majalisar bayan hutun makonni, ya yi kira da a dage zaman saboda rade-radin tsige shi.

Ya jingina dage zaman ne kan rantsar da zababbun mambobin da ake yi a halin yanzu.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa ya rawaito cewa wasu ‘yan majalisar sun kammala shirin tsige Femi Gbajabiamila saboda kakaba Tajudeen Abbas a matsayin dan takarar kakakin majalisar wakilai ta 10.

Wasu daga cikin ‘yan majalisar da suka zanta da manema labarai kan shirin tsigewar amma suka nemi a sakaye sunasu, sun yi zargin cewa kakakin majalisar ya dage zaman ne saboda tsoron za a tsige shi.

Mataimakin kakakin majalisar, Ahmed Wase, ya gaggauta sukar matakin na Femi Gbajabiamila, yana mai cewa dage zaman bashi da tushe balle makama amma aka yi watsi da batunsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: