Majalisa Ta Bukaci CBN Ya Saki $717,478,000 Na Kudaden Kamfanonin Jiragen Sama Da Suka Makale A Kasar

0 65

Majalisar dattawa a jiya ta bukaci babban bankin kasa, CBN, da ya saki dala miliyan 717 da dubu 478 na kudaden kamfanonin jiragen sama da suka makale a kasar.

Majalisar dattawan ta kuma yi kira ga bankin na CBN da ya ware dala miliyan 25 ga kamfanonin jiragen sama da ke aiki a Najeriya a gwanjon dallar da za ayi.

An cimma wadannan kudurori ne biyo bayan nazarin kudirin da Biodun Olujimi na PDP daga jihar Ekiti ya dauki nauyi a jiya a zauren majalisar.

Biodun Olujimi shine shugaban kwamitin majalisar dattawa akan harkokin sufurin jiragen sama.

Mataimakin shugaban kwamitin, Sanata Bala Na’Allah na jam’iyyar APC daga jihar Kebbi ne ya gabatar da kudirin a madadin Biodun Olujimi. Majalisar dattawan ta kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta gaggauta sauya yanayin yadda ake rikewa kamfanonin jiragen sama kudadensu a Najeriya.

Leave a Reply

%d bloggers like this: