Mataimakin Gwamnan Zamfara yace yana nan daram a jam’iyyar PDP

0 126

Mataimakin Gwamnan Zamfara Barista Mahdi Aliyu Gusau ya bayyana wa BBC matsayinsa, inda ya ce yana nan daram a jam’iyyarsa ta PDP bayan gwamna Bello Matawalle ya sauya sheka zuwa Jam’iyyar APC a jiya Talata.

Mahdi Aliyu Gusau ya kuma bayyana goyon bayansa ga matakin jam’iyyarsa ta PDP na garzayawa kotu domin ƙwatar kujerarta ta gwamna da kotun ƙoli ta najeriya ta ba ta, tare fatan mulki zai dawo hannunsa.

Duk da mataimakin gwamnan na Zamfara ya ce babu wata matsala tsakaninsa da gwamna Bello Matawalle amma ya ce gwamnan bai nemi shawararsa ba har zuwa lokacin da ya yi wanka zuwa jam’iyyar APC.

Leave a Reply

%d bloggers like this: