Mayakan ƙungiyar ISWAP sun kai hari ofishin ƴan sanda wanda yake ƙaramar hukumar Gujba ta jihar Yobe

0 140

Mayakan Kungiyar ISWAP sun kai hari Ofishin Yan sanda na Buni Yadi, wanda yake karamar hukumar Gujba ta Jihar Yobe.

A makon da ya gabata ne Rundunar Sojin Najeriya ta 27 wanda take aikin a yankin Arewa Maso Gabas, tare da tallafin sojojin Sama, suka hana Mayakan ISWAP shiga garin na Buni Yadi.

Amma wata Majiya ta fadawa manema labarai cewa mayakan sun kai harin ne a Ofishin yan sanda da kuma sabuwar barikin Sojoji wanda aka sake gyarawa kwanan nan.

Majiyar ta ce mayakan sun kai hari ne a lokacin da sukayi gangami, inda ta kara da cewa wasu yan sandan sun samu raunika wasu kuma sun tsere zuwa Daji.

Kazalika, an bada rahoton cewa mayakan sun kuma kone motocin sintirin yan sandan guda 2 da kuma wasu gine-gine a yankin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: