Mayakan RSF Sun Zargi Sojojin Kasar Sudan Da Kai Hare-hare Kan Tsohuwar Fadar Shugaban Kasar

0 100

Dakarun kungiyar RSF na Sudan sun zargi sojojin kasar Sudan da kai hare-hare ta sama kan tsohuwar fadar shugaban kasar da ke babban birnin kasar, Khartoum.

Mazauna birnin sun ba da rahoton tashin bama-bamai da yawa a yankin amma sojojin sun musanta ikirarin kungiyar ta RSF na cewa sun lalata fadar.

Mayakan kungiyar RSF sun ce za su mayar da martani mai tsauri.

Tsohuwar fadar tana kusa da kogin Nilu, kusa da sabuwar fadar da aka kaddamar a watan Janairun 2015.

Bangarorin biyu da ke gaba da juna dai na gudanar da tattaunawar zaman lafiya a kasar Saudiyya amma babu alamar samun ci gaba. Halin da fararen hula da suka makale a birnin ke ciki na ci gaba da tabarbarewa, inda likitoci suka ce ayyukan kiwon lafiya na daf da durkushewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: