Labarai

Mazauna karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara sun fara kauracewa gidajensu saboda fargabar hare-haren ramuwar gayya daga ‘yan fashin daji

Mazauna kauyen Mada a yankin karamar hukumar Gusau ta jihar Zamfara sun kauracewa gidajensu saboda fargabar karin hare-haren ramuwar gayya daga ‘yan fashin daji bayan kisan ‘yan sa kai 7 a ranar Lahadi, a abinda wasu suka kira harin ramuwar gayya.

Da suke tabbatar da lamarin, hukumomin ‘yansanda a jihar sun gayawa manema labarai a jiya cewa an aika da jami’an ‘yansanda zuwa wajen domin tabbatar da tsaron mazauna kauyen.

Wani mazaunin kauyen mai suna Yusuf Anka yace kwamandan ‘yan sa kai, Danmudi Na Mada, ya jagoranci abokan aikinsa zuwa kai hari maboyar ‘yan fashin daji inda suka kashe wani mashahurin dan fashin daji mai suna Mala’ikan Mutuwa.

Yusuf Anka yace kisan dan fashin dajin ya bakantawa ‘yan fashin daji lamarin da ya jawo ramuwar gayya.

Ana yabawa dan sa kan da aka kashe saboda tsare kauyukan Hausawa, musamman Mada da Wonaka, amma ana zarginsa da hannu a kisan Fulanin da babu ruwansu a yankin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: