Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya kalubalanci Gwamnatin Jihar Rivers kan kin amincewa da amfani da filin wasa A Port Harcourt

0 304

Ya ce masu shirya taron sun nemi izinin amfani da filin wasan domin taron da aka tsara yi a ranar Juma’a, amma gwamnatin jihar ta ki amincewa.

Wike ya yi wannan jawabi ne yayin da yake magana a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Captain Elechi Amadi, a lokacin kaddamar da masu kula da shirin Renewed Hope Agenda a kananan hukumomi da mazabun sanata na jihar.

Ministan ya gargadi gwamnatin jihar da cewa idan aka sake hana amincewa, masu shirya taron za su shiga filin wasan da karfi su gudanar da taron.

Ya ce filayen gwamnati mallakin al’umma ne, kuma be dace a hana ‘yan jihar amfani da su.

Kalamansa sun kara tayar da hankula a siyasar jihar Rivers yayin da ake shirin gudanar da karin ayyukan siyasa.

Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya kalubalanci Gwamnatin Jihar Rivers kan kin amincewa da amfani da filin wasa na Yakubu Gowon da ke Port Harcourt domin taron Renewed Hope Family.

Leave a Reply