Dan majalisar wakilai, Muktar Betara na jam’iyyar APC daga jihar Borno, mai neman kujerar kakakin majalisar wakilai ta kasa ta 10, ya tabbatar wa dukkan ‘ya’yan jam’iyyar da aka zaba a kowace jam’iyyar cewa za su samu wakilcin na adalchi idan aka zabe shi.
Muktar Betera ya bayar da wannan tabbacin ne a wani taro da ya yi jiya tare da wasu zababbun ‘yan majalisar a kasar Saudiyya.
A wata sanarwa da ya fitar bayan kammala taron, Muktar Betara, wanda shi ne shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar, ya gana da zababbun ‘yan majalisar da sauran masu ruwa da tsaki a ci gaba da gudanar da Umara a kasa mai tsarki.
Sanarwar ta ce taron ya samu halartar ‘yan majalisar wakilai da suka dawo da sabbin zababbun ‘yan majalisar wakilai daga jihohin Jigawa, Bauchi, Gombe, Adamawa, Katsina da Kaduna.
Sanarwar ta ce zababbun ‘yan majalisar a taron sun yi alkawarin marawa Muktar Betara baya tare da yaba wa ingancin shugabancinsa.
Sun kuma yaba masa bisa irin goyon bayan da ya baiwa mutanensa, ba tare da la’akari da addini, kabila ko jam’iyya ba.